Kenya: An sake bude Jami'ar Garissa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption yan sanda a kenya

Dalaibai sun soma karatu a Jami'ar Garissa ta kasar Kenya, inda 'yan bindiga suka harbe dalibai 148 a watan Afrilun bara sai dai ba dukkansu ne suka koma makarantar ba.

An girke jami'an tsaro a ciki da wajen Jami'ar, kuma mahukunta sun ce sun dauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin cewa mayakan Alshabab ba su sake kai hari Jami'ar ba.

Tuni aka yi wa dakin kwanan dalibai kwaskwarima.

Sai dai kusa da shi akwai wani aji da ake ganin gurbin da albarusai suka huhhuda.

Kawo yanzu dai daliban da suka nuna sha'awar dawowa karatun ba su taka kara sun karya ba, yawancinsu ma 'yan ajin kusa da na karshe ne da suka dawo don kammala shekara guda da ta rage musu.