Yunkurin rage mutuwar aure a Kano

Image caption amare yan mata

A wani mataki na rage yawan mutuwar aure a kasar Hausa, wata kungiyar Musulmai a jihar Kano ta bai wa 'yan mata horo kan yadda za su yi hulda da mazansu idan sun yi aure.

Cibiyar addinin Musulunci mai suna Asusun Bin Bazz ta ce matsalolin da yawan mace-macen auren ke haddasawa suna da dumbin yawa don haka akwai bukatar samo hanyoyin magance matsalar.

Shugaban cibiyar, Sheikh Abdulwahab Abdallah, ya shaida wa BBC cewa sun kwashe makonni shida suna nunawa 'yan matan dabariun zaman aure, cikinsu har da tsafta da iya girki, yana mai cewa yawancin matan suna kallon maza a matsayin makiyansu da zarar sun yi aure shi ya sa ake samun matsaloli.

'Yan matan dai sun shaida wa BBC cewa sun gamsu da irin horon da suka samu.