EFCC: PDP na goyon bayan bincike

Tutar jam`iyyar PDP a Najeriya
Bayanan hoto,

Tutar jam`iyyar PDP a Najeriya

Jam'iyyar PDP a Najeriya ta bukaci hukumar EFCC ta ci gaba da kama mambobinta da ake zargi da hannu wajen karbar kudin sayen makamai.

Sai dai Barrister Jallo, a hirar sa da Yusuf Tijjani ya ce bai kamata a dorawa Goodluck Jonathan alhakin badakalar sayan makaman ba, yana mai cewa zargin da ake yi wa wasu 'ya'yan jam'iyyar ba zai shafi martabar jam'iyyar ba:

Barrister Jallo ya kuma bukaci hukumar EFCC ta daure duk dan jam'iyyar PDP da kotu ta tabbatar ya ci moriyar kudin sayen makaman.

Ya kara da cewa kashi tamanin bisa dari na 'yan jam'iyyar PDP mutanen kirki ne, yana mai cewa bai kamata a dinga yi wa 'ya'yan jam'iyyar kudin-goro a kan zargin sama-da-fadi da kudaden kasa ba.

A halin da ake ciki dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC na tuhumar wasu ya 'yan jam'iyyar da suka hada da tsohon shugaban PDP na kasa, Ahaji Bello Haliru da Kakakin jam'iyyar Olisa Metuh da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa kan wannan badakalar.