Za a kai agajin abinci ga mutanen Madaya

Image caption Jami`an Majalisar dinkin duniya dauke da abinci da magunguna sun nufi garin Madaya inda mutane ke mutuwa saboda yunwa.

Majalisar Dinkin duniya ta ce a yau Litinin ne ake sa ran wani ayarin jami'anta dauke da abinci da magunguna zai kama hanyar zuwa garin Madaya da aka yi wa kawanya a Syria.

Rahotanni na cewa kimanin mutum dubu Arba'in ne aka yi wa kawanya a garin, sakamakon rufin-gangar da sojojin gwamnatin Syriar suka yi wa garin, kuma ba a sake shigar da abincin garin ba tun watan Oktoban da ya wuce.

Majalisar dinkin duniyar ta ce ta samu labarin cewa akwai mutanen da yunwa ta kashe a garin.

Melissa Fleming, jami'a ce ta hukumar da ke kula da masu gudun-hijira ta majalisar dinkin duniyar.

Ta ce, "Tun daga lokacin da aka fara wannan yakin, an yi ta amfani da salon azabta mutane da yunwa a garuruwa da birane, an kuma yi wa yankuna kawanya, kuma al'umomin da ake ritsawa da su na sha wahala kwarai da gaske."

A makon jiya ne gwamnatin Syria ta amince za ta kyale ayarin majalisar dinkin duniyar ya shiga garin.

Haka kuma za a kai kayan agajin wasu garuruwa biyu da 'yan tawaye suka yi wa zobe a lardin Idlib.