Masu amfani da Explorer na fuskantar hadari

Image caption Explorer

Kimanin mutum miliyon 340 da ke amfani da tsofaffin manhajojin Explorer

Kamfanin Microsoft ya dakatar da hidimar da yake yi wajen tallafawa da yin kariya ga masu amfani da tsofaffin manhajojin Explorer wajen shiga intanet.

Kamfanin ya ce sauye-sauyen za su shafi manhajar Explorer ta 8 da ta 9 da kuma ta 10 kamar yanda kamfanin ya sanar a watan Agustan 2014.

Wasu dai na ganin cewa masu amfani da tsofaffin manhajojin Explorer sun kai kashi 20 bisa dari na masu shiga intanet, yayin da kashi 55 bisa dari ke amfani da sabuwar manhajar Explorer, kamar yanda Computerworld ke ikirari.

Masu kutse a shafukan intanet kan yi amfani da mashiga irin Explorer wajen yin aika-aikarsu.

Daga ranar Talata, 13 ga watan Janairin wannan shekarar ne sabuwar manhajar Explorer ta fara aiki, kuma masu amfani da ita za su samu tallafi da kariya daga kamfanin Microsoft.

Kamfanin dai ya shawarci masu shiga intanet da su sabunta manhajar Explorer domin ta fi saurin sarrafawa da samun sukunin shiga intanet, ga kuma kariya daga masu kutse.