Guantanamo: Mahama ya kare matsayinsa

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Shugaba Mahama ya ce ba biyan shi aka yi ba

Shugaban kasar Ghana, John Mahama, ya kare shawararsu ta karbar Yamanawa biyu da aka saki daga kurkukun sojin Amurka na Guantanamo.

A makon jiya ne ma'aikatar tsaron Amurka ta ba da sanarwar mayar da mutanan biyu zuwa Ghana bayan sun shafe sama da shekaru 10 suna tsare a wajen.

Shugaba Mahama ya ce ba bu wani kudi da aka baiwa Ghana domin ta karbe su kuma ba wata barazanar tsaro tattare da su.

Shugabannin addinin Kirista sun bayyana fargabarsu game da sha'anin tsaron kasar, kuma babbar jam'iyyar adawa ta NPP ta ce ya kamata a ce an tuntubi jama'ar kasa game da matakin.