Bam ya hallaka mutane 10 a Istanbul

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu rahotanni sun ce 'yan kunar-bakin-wake ne suka tayar da bama baman.

Hukumomi a kasar Turkiyya sun ce mutane akalla 10 ne suka mutu bayan wasu bama- bamai sun tashi a wani yanki da masu yawan bude ido suka fi zuwa da ke birnin Istanbul.

Bama baman sun fashe ne da misalin karfe 10 na safe a agogon kasar a yankin Sultanahmet kusa da Blue Mosque.

Wani bayani da aka wallafa a shafin intanet na gwamnan birnin ya ce mutane 15 ne suka jikkata.

Wasu rahotanni sun ce 'yan kunar-bakin-wake ne suka tayar da bama baman ko da ya ke ba a tabbatar da rahotannin ba.

'Yan sanda sun killace wurin da lamarin ya faru.