Takardun kasafin kudin Nigeria sun yi layar zana ?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A bara shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin

Rahotannin daga majalisar dattijan Najeriya na cewa takardun kasafin kudi na Najeriya na 2016 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar dokokin sun bace.

Wani dan majalisar dattawan Najeriya ya shaida wa BBC cewa ba a san inda takardun kasafin kudin suka shiga ba.

A ranar 22 ga watan Disambar bara, shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin, wanda shi ne mafi yawan kudi a tarihin Najeriya.

Wata majiya a majalisar kuma cewa ta yi ana zargin takardun kasafin kudin sun bace ne tsakanin wasu ma'aikatan majalisar dokokin kasar.

Bayanai sun ce 'yan majalisar dokoki sun nemi su boye batun bacewar takardun saboda gudun abin kunya, amma kuma sai aka samu wadanda suka kwarmata labarin.

Bacewar takardun kasafin kudin zai iya cikas ga ayyukan da aka sa a gaba na gwamnatin kasar, musamman wasu sauye-sauye da gwamnatin Shugaba Buhari ke shirin aiwatarwa.

'Rudani'

Mallam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaba Buhari, ya shaida wa BBC cewa, "babu wanda yake da ikon janye kasafin kudin daga majalisa idan ba shugaban kasa ba, kuma a iya saninsa shugaban kasar bai janye kasafin kudin ba."

A ranar Talata shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki ya yi wata ganawa da shugaba Buhari, kuma Garba Shehu ya ce ba shi da masaniyar ko ganawar tana da alaka da batun bacewar takardun kasafin kudin domin a cikin sirri suka yi ganawar.

Sai dai a nasa bangaren, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar wakilan Najeriya Abdurrazak Namdas, ya shaida wa BBC cewa, su nasu takardun kasafin kudin suna nan babu abinda ya same su.

Ya kuma kara da cewa a ranar Laraba za su fara raba takardun kasafin kudin ga 'yan majalisar wakilai domin su fara nazari a kai kafin a fara muhawara a kansu.