Obama ya karfafa wa Amurkawa gwiwa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Brack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya karfafa wa Amurkawa gwiwa a jabinsa na karshe da ya yi wa majalisun dokokin kasar a matsayinsa na shugaban kasa.

Ya ce Amurka za ta karfafa fiye da da idan ta rungumi sauyi, kana ya bukaci 'yan majalisar su guji son zuciya ta yanda Amurka za ta samu ci gaba na hakika.

Shugaba Obama ya ce zai kaddamar da sabon shirin yaki da cutar sankara ko daji.

Haka kuma ya ce zai yi kokari wajen kare makomar Amurka ta fuskar makamashi ta hanyar matsa-kaimi wajen daina amfani da makamashi mai illa ga muhalli.

Dangane da batun tsaro kuwa, Mista Obama cewa ya yi Amurka za ta ci gaba da farautar 'yan ta'adda, kana ya bukaci majalisun dokokin kasar da su amince wa gwamnati yin amfani da karfin soji wajen yakar kungiyar IS.

Kazalika shugaban Amurkar ya bukaci majalisar kasar ta cire takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba wa Cuba, yana kuma alwashin cewa zai dage wajen ganin an rufe sansanin Guantanamo.