Wace ce 'Rosa Parks' din Saudiyya ?

Hakkin mallakar hoto Nawal alHaws awi

Nawal al-Hawsawi mace ce mai kaifin-baki, bakar fata, kwararriyar mai tuka jirgin sama, kuma ta auri farar-fata - masu suka a kasar ba sa son mace ta yi dukkan abubuwan da ta yi.

Sai dai duk da zage-zagen da take sha a shafukan sada zumunta na zamani, ba ta damu ba. Hasalima tana nuna kauna ga duk wanda ya zage ta.

Al-Hawsawi ta zama taurariya a shafukan sada zumunta. Tana da mabiya 50,000 a shafinta na Twitter, inda take wallafa bayanai kan muhimmancin zamantakewa tsakanin mutanen da ke da bambancin launin fata, da bai wa kowa dama ya auri wanda yake so.

Sai dai ba dukkan mutanen da ke karanta sakonninta ne ke goyon bayanta ba.

A watan Disamba ta sha zagi da nuna wariyar launin fatar da ba ta taba sha ba.

Masu zagin nata sun rika aika mata da hotunan gwaggwan birrai, inda suke kwatanta ta da su, sannan suka rika yin kalaman batanci inda suke ,kiranta baiwa.

Al-Hawsawi ta girmanne a birnin Makka, kuma har lokacin da ta tafi Amurka ba ta taba tunanin za a nuna mata wariyar launin fata ba.

A Amurka ne ta koyi tukin jirgin sama, inda ta kware sosai, ko da ya ke har yanzu a kasar ta ba a ba ta izinin tuka jirgin ba.

Haka kuma ta karancin ilimin bai wa ma'aurata shawara kan yadda za su inganta aurensu, wanda shi ne sana'arta a yanzu.

Al-Hawsawi ta auri wani Ba'amurke, sannan ta koma Saudiyya shekaru kadan da suka wuce, inda daga nan ne ta fara fuskantar kalubale.

'Tana shan zagi'

Wata mata ta zazzage ta a ranar da ake bikin samun 'yancin Saudiyya a shekarar 2013.

Nuna wariyar launin fata babban laifi ne a kasar, don haka ne ma ta kai matar kara a kotu.

Sai dai ta amince ta janye karar bayan matar da ta zage ta, ta ba ta hakuri, inda a yanzu suka zama kawaye.

Wannan labarin ya ja hankalin kafafen watsa labarai na kasar, kuma al-Hawsawi ta rika shiga gidajen talabijin inda ta rika yin bayani a kansa.

Kafafen watsa labaran Saudiyya sun sanya mata suna "Rosa Parks" din Saudiyya - wato suna kwatanta ta da matar nan da ta yi fafutikar kare hakkin dan adam ta Amurka.

Al-Hawsawi ta rika yin amfani da shafin na Twitter wajen yin kiraye-kiraye a daina nuna wariyar launin fata.

Haka kuma tana amfani da shafin wajen yin yaki da masu muzgunawa mata da nuna kiyayya ga bil adama da nuna wariyar launin fata.

Sai dai wadannan kiraye-kiraye da take yi sun harzuka wasu 'yan kasar, musamman masu tsattsuaran ra'ayi.

Ta shaida wa Sashen Ingili na BBC Trending cewa, "Ba sa son abubuwan da nake fada a kan aure da hadin kai da ingantacciyar rayuwa. Sun rika wallafa hotunan miji da na 'ya'yana, suna kiran mutane su yayata su. Hakan ya bata min rai".

Sai dai duk da haka Al-Hawsaw ta ce ba za ta karaya ba, tana mai cewa tana koyi ne da mutane irinsu Mandela, MLK da Gandhi, wadanda suka jajirce wajen ganin duniya ta daina nuna wariyar launin fata.