Kwamiti ya bukaci a hukunta sojojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto NIGERIA GOVT
Image caption sojojin najeriya

Kwamitin da rundunar sojin Najeriya ta kafa don binciken jami'anta da ake zargin sun aikata ba daidai ba a lokacin zaben shekara ta 2015 ya mika rahotonsa.

Kammalallen rahoton na dauke da bayanai da aka tattaro da suka kunshi abubuwa da dama.

Shawarwarin da kwamitin ya bayar sun hada da ritayar dole ga wasu jami'an sojin da aka samu da aikata laifi.

Kazalika wadanda suka yi kokari wajen samar da bayanai game da lamarin za su samu yabo na masamman.

Duk wanda aka samu da aikata ba daidai ba za a yi masa hukunci daidai laifin shi, in ji rahoton kwamitin.