Apple zai kera mota mai aiki da lantarki

Image caption tesla car

Elon Musk shugaban kanfanin Tesla ya sanar da cewa ba wani siri ba ne kanfanin zai kera irin wannan motar.

Shugaban kanfanin ya kara da cewa nan da wani lokaci duk motar da ba ta iya tuka kanta za ta zama tsohon ya yi.

Kanfanin na Tesla da hadin gwiwar kanfanin Nissan da na BMW zai kasance kanfani da ya fi sayar da motoci masu aiki da lantarki.

To sai dai yanzu kanfanin ba ya samun wata riba .

Wani kalubale da ya ke fuskanta a 'yan watannin baya-bayan nan shi ne hayar da dama daga cikin injiniyoyin shi da wasu kanfanoni abokan hamaya suka yi.

Apple dai bai sanar da cewa ya fara aikin kera irin wannan motar ba, duk da cewa ya yi rajistar wasu motoci da aikinsu ke da alaka da intanet, wadanda suka hada da Apple.car da kuma Apple.auto.