An bukaci a kwashe mutane daga Madaya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ma'aikatan majalisar sun kai kayan abincin da za su yi makonni hudu ba su kare ba.

Majalisar dinkin duniya ta ce mutane 400 da aka yi wa kawanya a garin Madaya na kasar Syria na fuskantar yiwuwar mutuwa idan dai ba a yi gaggawar fitar da su daga garin ba.

Shugaban hukumar bayar da agaji ta Majalisar, Stephen O'Brien, ya ce mutanen na fama da matsananciyar yunwa da rashin magunguna.

Wani ayarin ma'aikatan majalisar ya isa garin dauke da kayan abinci da magunguna da za su kai makonni hudu ba su kare ba, bayan an kwashe tsawon lokaci ana yi wa mutanen garin kawanya.

Hukumar ta ce jami'anta sun ga kananan yaran da ke fama da yunwa a garin Madaya, lokacin da suka kai kayan agaji can ranar Litinin.

'Musanta Zargi'

Ya ce babu karya a cikin hotunan da aka nuna na mazauna garin da yunwa ta yi wa illa, kuma mutanen garin na cikin mawuyacin hali.

Gwamnatin Syria dai ta musanta zargin da ake yi cewa tana amfani da salon azabtar da mutane da yunwa a matsayin dabarar yaki.

Kazalika, an jagoranci jami'an majalisar dinkin duniyar zuwa wasu garuruwa biyu na magoya bayan gwamnati da 'yan tawaye suka yi wa kawanya.

Mazauna garin Madaya sun yi bayani a kan halin kuncin rayuwar da suka samu kansu ciki, sakamakon kawanyar da aka yi wa garin nasu.

Da dama daga ciki sun ce wuya ta saka su cin ciyawa, yayin da wasu kuma suka yi ta bin juji suna kalen abin kalaci.