Cin dankali yana haifar da ciwon-suga

Hakkin mallakar hoto MEHR
Image caption Masanan sun ce sitatin da ke cikin dankali na kara yawan suga a cikin jini.

Wasu masana kimiyya a Amurka sun ce mata masu juna-biyu da ke yawan cin dankali za su fuskanci hadarin kamuwa da ciwon-suga ko diabetes.

Masanan sun yi nazari ne a kan mata masu ciki dubu 21,000, kana suka fahimci cewa mata masu juna-biyu da ke cin dankali kwaya biyar ko fiye a mako na cikin hadarin kamuwa da ciwon-suga da kashi 50 bisa dari.

Sun bayyana cewa sitatin da ke cikin dankali na kara yawan suga a cikin jini.

A cewar masanan ciwon sugar mata masu juna biyu kan yi sauki bayan haihuwa, amma hadarinsa kan shafi iyaye mata da ta jariransu bayan wani lokaci mai tsawo.