Mahamadou Issoufou zai fuskanci kalubale

Hakkin mallakar hoto
Image caption Cheiffou Amadou

Dan takarar jam'iyar RSD Gaskiya a zaben shugaban kasar Nijar Malam Shehu Amadu ya ce zai yi wuya shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya lashe zaben tun a zagaye na farko.

Ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da masu goyon bayan Shugaba Issoufou keikirarin cewa za su lashe zaben a zagayen farko.

Ga al'ada a kan kai ga zagaye na biyu ne kafin a tantance wanda zai ci zaben.

A wannan karon ma Shehu Amadou na ganin cewa zaben zai kai ga haka, don babu wani babban canji ga jam'iyun siyasar da ka iya tabbatar da cin zaben tun zagaye na farko.