Kotu ta halalta leka sirrin ma`aikatan Birtaniya

Image caption Private message

Kotun Tarayyar Turai da ke hukunta laifukan tauye hakkin bil'adama ta halalta wa shugabanni ko masu kamfani duba sirrin ma'aikatansu ta adireshi ko shafukansu na intanet a lokacin aiki.

Kotun ta ce za su iya karanta hirarrakin da ma'aikata ke yi ta manhajar Yahoo Messenger da sauran dangoginta, muddin suka yi hirarrakin a lokacin aiki.

A cewar Alkalan kotun, ma'aikaci ba shi da hurumin shiga hira da wani a kan wata harkar da ba ta shafi aikinsa a lokacin aiki ba, saboda haka shugabanni suna da hurumin leka shafukan hirarrakin da ma'aikatansu ke yi don kare aiki da sirrin ma'aikatun nasu.

Alkalan, wadanda suka yi zama a Strasbourg sun yanke wannan hukuncin ne a ranar Talatar da ta wuce, suna jaddada cewa sa ido a kan abubuwan da ma'aikata ke yi zai taimaka wajen hana su shiga wata sabgar da ba ta shafe su ba.

Kuma wannan hukuncin ya shafi dukkan kasashen da ke kungiyar Tarayyar Turai, kenan wajibi ne su martaba shi.

Wani Injiniya dan kasar Romania mai suna Bogdan Barbulescu ne ya kai karar shugabansa a wani kamfani yana zargin cewa ya keta haddinsa, ya leka masa sirri sakamakon karanta wasu sakonninsa da ya yi ta intanet, har ta kai ga sallamar Injiniyan daga aiki a shekara ta 2007.

Shugaban nasa dai ya gano cewa Injiniyan na amfani da adireshinsa na Yahoo Messenger yana tura wasu sakonninsa da ba su shafi aiki ba.

Da ma kamfanin ya haramta wa ma'aikatansa tura wasu sakonnin kashin-kansu a lokacin aiki.