'Yan Boko Haram na boye bam a baro - Sojoji

Hakkin mallakar hoto boko haram
Image caption Shekau ya yi layar zana

Rundunar tsaron Najeriya ta ce a yanzu 'yan Boko Haram sun soma bin wata hanyar yaudara ta saka bam a cikin baro na kayan lambu.

Cikin watan sanarwa da kakakin rundunar, Birgediya Janar Rabe Abubakar ya sanya wa hannu, ta ce 'yan Boko Haram sai su saka abubuwan fashewa a baro, sannan su shiga cikin jama'a kafin su tayar da bam din.

Rundunar ta ce wannan salon na 'yan Boko Haram ya biyo bayan nasarar da sojoji suka yi na kawar da 'yan kungiyar daga manyan garuruwa a arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta ce ya kamata jama'a su farga domin kare kansu daga fadawa tarkon 'yan Boko Haram.

A wani mataki na murkushe 'yan Boko Haram din, rundunar ta sanar da daukar sabbin sojoji 12,000 aiki a wannan shekarar.