Buhari zai binciki sace 'yan matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwanaki 600 kenan da sace 'yan matan Chibok

Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umurnin a gudanar da bincike kan sace 'yan matan sakandiren Chibok a jihar Borno su 219 da 'yan Boko Haram suka sace.

Nan ba da jimawa ba ne ba dai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro , Janar Babagana Munguno zai kafa Kwamitin da zai binciki lamarin da ya faru a watan Afrilun 2014.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar bayan ganawar da shugaban Muihammadu Buhari ya yi da wasu daga cikin iyayen yaran da kuma 'yan kungiyar Bring Back Our Girls a fadarsa da ke Abuja.

Iyayen 'yan matan tare da masu mara musu baya ne cikin yanayi mai sosa rai, suka yi maci a Abuja, a yayin da aka cika kwanaki 600 da 'yan Boko Haram suka sace daliban.

Wasu daga cikin iyayen, sun fusata inda suka zauna a tsakiyar titi suna ta kuka.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a wani bidiyo da ya fitar 'yan makonni bayan sace 'yan matan, ya yi barazanar 'sayar' da su.