Iyayen 'yan matan Chibok sun yi maci a Abuja

Image caption Kwanaki 600 iyayen ba su ga 'ya'yansu ba

Daruruwan iyayen 'yan matan Chibok wadanda aka sace a makarantarsu ne, suka yi maci a Abuja babban birnin Najeriya.

Iyayen tare da masu mara musu baya ne cikin yanayi mai sosa rai, suka yi macin a yayin da aka cika kwanaki 600 da 'yan Boko Haram suka sace daliban.

Sun yi maci ne zuwa fadar shugaban Najeriya, domin su gana da shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya girgiza su, bayan da ya bayyana cewa babu kwakkwarar shaidar da ke nuna inda 'yan matan Chibok din suke.

Wasu daga cikin iyayen, sun fusata inda suka zauna a tsakiyar titi suna ta kuka.

Image caption Iyaye maza sun kasa daure wa

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a wani bidiyo da ya fitar 'yan makonni bayan sace 'yan matan, ya yi barazanar 'sayar' da su.