An kai harin bama-bamai a Jakarta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lamarin ya faru ne a kusa da ofishin majalisar dinkin duniya.

An kawo karshen harbe-habe da fashewar bama-bamai da suka rika tashi a Jakarta, babban birnin Indonesia.

Bama baman sun tashi ne a wani rukunin shaguna da ke kusa da fadar shugaban kasa da kuma ofishin Majalisar Dinkin Duniya.

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane bakwai, cikinsu har da maharan guda biyar.

Wasu rahotanni sun ce an kama maharan guda uku.

Da ma dai 'yan sanda sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar kai wa kasar hari, kuma sun yi kira a kara matakan tsaro.

Shugaban kasar Joko Widodo ya ce ba za su bai wa 'yan ta'addda kai bori ya hau ba, yana mai yin kira ga 'yan kasar da su ci gaba da jajircewa wajen ganin an kawar da 'yan ta'adda.