Zazzabin lassa ya bulla a Abuja

Hakkin mallakar hoto Prof S.R. Belmain University of Greenwich
Image caption Beraye ne ke haddasa cutar.

Ministan lafiya na Najeriya ya ce zazzabin lassa mai saurin kisa ya bulla a Abuja, kuma tuni ya kashe mutum daya.

Wata sanarwa da ofishin ministan, Isaac Adewole, ya fitar ta ce mutumin da ya mutu ya kamu da cutar ne a birnin, inda aka garzaya da shi babban asibin kasa da ke Abuja, kuma a can ne rai ya yi halinsa.

Ya kara da cewa mutumin, mai shekara 33, dan asalin Jos ne wanda ya yi aure kwanan nan sannan ya koma zama a yankin Kubwa da ke Abuja.

Ministan ya ce ya bayar da umarni a bai wa mutanen da mutumin ya yi hulda da su kafin ya mutu kulawar gaggawa domin ganin ko sun kamu da ita.

Hakan dai ya kawo adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar zuwa 43 a jihohi goma na kasar.

Ana kamuwa da cutar ne dai ta hanyar mu'amala da berayen da ke dauke da ita.