Farashin fetur na ci gaba da faduwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Farashin man ya fadi ne bayan wani rahoton da ke nuna cewa man da Amurka ke ajiyarsa ya karu.

Farashin gangar mai ya sake faduwa kasa warwas kasa da dala 30 , faduwar da bai taba yin irin ta ba a cikin shekara 12 da suka wuce, lamarin da ya haddasa mummunar faduwar farashin hannayen-jari a Amurka da Asiya.

Farashin man dai ya fadi ne bayan wani rahoton da ke nuna cewa man da Amurka ke ajiyarsa ya karu.

Babban dalilin faduwar farashin man dai shi ne labarin da aka samu na karuwar man da Amurka ke ajiyarsa, alamar da ke nuna cewa matutan man kasar ba za su bukaci danyen mai sosai ba a nan kusa.

Har wa yau, masana na cewa watakila farashin ya sake dungurawa idan kasar Iran ta fara shigar da nata man kasuwannin duniya, wato lokacin da aka cire mata takunkumin tattalin arziki.