Al-Shabab ta kwace iko da sansanin AMISON

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al-Shabab ta kashe sosjojin Kenya 60.

Kungiyar al-Shabaab ta ce karbi iko da a wani sansanin sojin kungiyar tarayyar Afirka a kudancin Somalia kusada kan iyaka da kasar Kenya.

Rundunar kiyaye zaman lafiyar ta tarayyar Afirka a Somalia, AMISON ta ce an kai wa sojojinta hari amma ta musanta cewa 'yan bindiga sun kwace sansanin.

Wasu mazauna garin El Adde sun ce an kashe sojojin Kenya da dama, wasu kuma sun tsere.

" Mun ji karar fashewar wani abu mai karfi daidai misalin karfe biyar da rabi na safe. Sannan sai kuma muka ji munanan harbe-harben bindiga sun biyo baya. Al Shabab ta ce ta kashe sojojin Kenya sittin ta kuma kwace motocin sojin da kuma makamai," in ji mutumin.

Bayanai sun ce an kashe sojojin Kenya fiye da 60 da ke wajen.