An dakatar da wani coci kan luwadi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kiristoci da dama suna adawa da auren jinsi guda.

Majami'un Anglikan a duniya sun dakatar da majami'ar Episcopal mai bin darikar Anglikan a Amurka ta Arewa daga shiga cikin ayyukansu na bushara, saboda amincewa da ta yi da auren jinsi guda.

Shugabannin majami'un Anglikan da suke taro a Canterbury, sun ce aure wani hadi ne da ake yi tsakanin jinsin mace da na miji, don haka majami'ar ta Episcopal ta kauce daga koyarwar da akasarin mabiya darikar Anglikan suka yarda da ita.

An dakatar da majami'ar ce na wucin gadi, saboda gudun kawo rabuwar kai tsakanin mabiya darikar Anglikan din a kan batun aure tsakanin jinsi guda.

Mabiya darikar ta Anglikan, musamman a kasashen Afrika suna suka auren jinsi guda.