Ebola ta sake kunno kai a Saliyo

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 11,000 a kasashen Guinea da Liberiya da Saliyo.

Jami'an lafiya a Saliyo sun tabbatar da mutuwar wani mutun da aka samu dauke da cutar Ebola, bayan 'yan wasu sa'o'i da hukumar lafiya ta duniya ta bayyana kasar a matsayin wacce ta kawar da cutar baki daya.

Hukumomi a Freetown babban birnin kasar sun ce bincike ya nuna cewa wani mara lafiya da ya mutu a arewacin gundumar Tonkolili, ya kamu da cutar Ebola.

Da ma a lokacin da hukumar lafiyar ta duniya ke sanar da kawo karshen cutar Ebolan a Saliyo ranar Alhamis, kwamishinan kula da cutar na Tarayyar Turai ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar a sake samun barkewar cutar.

Cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 11,000 a kasashen Laberiya da Guinea da Saliyo, tun bayan barkewar ta shekaru biyu da suka gabata.