Shi'a: An yi taron sojoji da malamai

Image caption Janar Tukur Burutai

A Najeriya, rundunar sojin kasar a jihar Kaduna gana da malaman addinin Islama domin kara musu haske game da abinda ya wakana, a lokacin da sojojin kasar suka yi arangama da 'yan Shi'a a Zaria, kwanakin baya.

Rundunar sojin dai na ganin wasu jama'a a kasar, ba su fahimci irin hakurin da sojojin suka nuna ba, sannan kuma, ba su san irin tanadin da kungiyar ta Shi'a ta yi ba kafin arangamar.

Kwamandan runduna ta daya ta sojin daka Kaduna, Manjo Janar Adeniyi Oyebade ya ce inda 'yan kungiyar ta Shi'a ba sa take wa wasu mutane hakkokinsu, da arangamar ba ta auku ba.

Ya ce rundunar sojin kasar ba za ta bar wani ya rika daukan doka a hannunsa ba.

Daya daga cikin malaman da suka halarci taron, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya bukaci gwamnati da ta rika daukan shawara daga malaman addinai.

Ya ce matsalolin ayyukan kungiyoyi iribsu Boko Haram da 'yan Shi'a, an dage ana bai wa gwamnati shawarori a kansu kafin su ta so.