Taiwan na gudanar da zabe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jam'iyyar hammayar kasar Taiwan tana fatan babban nasarar da ba a taba gani a kasar ba.

Ana gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Taiwan, inda batun dangantakar kasar da China ya ke kan gaba a wurin masu kada kuri'a.

Jam'iyyar KMT mai mulki a Taiwan din wacce ke son kasar ta sake hade wa da China, ta na fuskantar babban kalubale daga jam'iyyar DPP mai son kasar ta ci gaba da cin gashin kanta.

Sakamakon jin ra'ayin jama'a ya nuna 'yar takarar jam'iyar adawa ce, ke kan gaba, wacce take da ra'ayin a bar jama'ar Taiwan din su zaba ma kansu abin da suke so, game da dangantakar kasar da China.

China ta na nuna tana cewa ta na iko da Taiwan din, tun da aka kawo karshen yakin basasar