Kutse ne ya katse lantarki a Ukraine- Amurka

Image caption Tashar samar da lantarki a Ukraine

Ma'aikatar tsaron cikin gida a Amurka ta ce ayyukan masu kutse ne suka janyo katsewar wutar lantarki a yammacin Ukraine a cikin watan jiya.

Kutsen ya sa lantarki ta yanke wa mutane dubu 80 masu amfani da na'urar lantarki ta Prykarpattyaoblenergo a arewacin Ukraine.

Masana sun bayyana lamarin a daukewar lantarki da kasar ta fuskanta na farko da masu kutse suka yi sanadin sa.

Hukumar tsaro ta farin kaya a Ukraine ta ta'allaka kusten da aikin mahara da Rasha, inda suka zargi gwamnatin Rasha da daukan nauyin shi.

Ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta ce manhaja mai cutar wa da aka yi amfani da ita wajen kutsen, "BlackEnergy Malware", an sakala ta ne a cikin wani sako da aka goya a jikin manhajar Microsoft Word.

Irin wannan matsalar ce aka gano a a shekarar 2014 a wasu na'urorin Amurka, sai dai ba su haifar da katsewar lantarki a Amurkan ba.