Lassa: An rufe wani asibiti a Lagos

Hakkin mallakar hoto thinkstock

A Najeriya, hukumomi a jihar Lagos suna sa ido a kan wani asibitin kudi da suka rufe a yankin Ojokoro, inda wani mutun na farko da aka samu ya kamu da cutar zazzabin Lassa a jihar, ya fara zuwa domin a duba lafiyar sa.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Jide Idris ya ce ana sa ido a kan wasu marasa lafiya dake cikin asibitin su 15, da kuma wasu ma'aikatan lafiya a asibitin su 25 har na tsawon kwana 21.

An samu cutar ta Lassa wacce ke samo asali daga beraye a tare da wani dalibi mai shekaru 25 a jihar ta Lagos, wanda yanzu haka ake masa magani a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Lagos.

Dr. Idris ya ce ana kokarin gano mutanen da dalibin yayi mu'amala dasu har ma a asibitin koyarwa na jami'ar.

Cutar zazzabin Lassa ta kashe fiye da mutane 40 a Najeriya sakamakon barkewarta a wasu jihohin kasar.