Taiwan:An zabi mace shugaba a karon farko

Hakkin mallakar hoto Getty

Sabuwar shugabar kasar Taiwan Tsai Yingwen ta ce wajibi ne a daraja tsarin dimokradiyya da kuma martabar tsibirin a matsayinsa na kasa.

To amma ta ce za ta yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a dangantaka da China.

A martaninsa na farko ofishin kula da harkokin Taiwan dake China yace zai ci gaba da yin adawa da dukkan wani shirin Taiwan na ayyana yancin kai.

Wakilin BBC a Taipei yace nasarar Tsai Yingwen ya kara kambama fargaba a Taiwan cewa tsibin na nema yin dogaro baki daya a kan China ta fuskar tattalin arziki wanda dama China na kallon Taiwan din a matsayin yankinsa da ya balle.