Shi'a:El-Rufa'i ya kafa kwamitin bincike

Hakkin mallakar hoto kaduna govt

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da kafa kwamitin binciken rikicin da ya faru tsakanin kungiyar yan Shi'a a Najeriya da kuma sojoji a cikin garin Zaria a watan da ya gabata.

A cikin wata sanarwa a ranar Asabar din nan wadda kakakin gwamnan Samuel Aruwan ya sanyawa hannu, Gwamna jihar Kaduna Nasir el-Rufa'i yace za'a kaddamar da mambobin kwamitin a mako mai zuwa.

Kwamitin na da Justice Mohammed Lawal Garba a matsayin shugaba.

Ana sa ran kwamitin bayan kaddamar da shi ya mika rahotonsa cikin makonni shida.

Kwamitin zai binciki musababbin rikicin da tantance mutanen da aka kashe ko aka ji wa rauni ko kuma suka bace a lokacin tarzomar.

Hakan nan kuma kwamitin zai binciki rawar da wasu mutane da hukumomi na tarayya da na jihohi suka taka domin tantance ko matakan da suka dauka sun zama wajibi ko sun dace a yanayin da lamarin ya faru.