Nigeria: Hukumar sake gina arewa maso gabas

Hakkin mallakar hoto

A Najeriya, Majalisun dokokin tarayyar kasar sun bullo da wani kuduri na kafa wata hukuma ta musamman domin raya yankin arewa maso gabashin kasar wanda rikicin Boko Haram ya lalata.

Dubban mutane ne rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriyar ke ci gaba da tagayyarawa.

A kwanakin baya ne aka gabatar da kudurin dokar a gaban majalisun, amma daga bisani aka dai na jin duriyar batun.

Sanata Ali Wakili, da ya fito daga yankin, ya ce yana fatan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sanya hannu a dokar idan majalisun suka kammala aiki akanta.

Yankin arewa maso gabashin Najeriyar ya shafe shekaru da dama ya na fama da tarzomar Boko Haram.