Iran ta sa fetur na ci gaba da faduwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Farashin man fetur ya yi kasa da dala 28 a yau Litinin, a kasuwannin duniya.

Farashin man fetur ya ci gaba da faduwa kasuwanni a ranar Litinin, bayan kasashen duniya sun cire takunkumim da suka kakaba wa kasar Iran.

Yanzu dai farashin man ya sauka kasa da dala ishirin da takwas ga kowacce gangar mai daya a karo na farko tun shekarar 2003, kafin daga bisani kuma ya farfado kadan.

Masu sharhi sun ce damar da Iran ta samu ta kara shiga kasuwannin duniya za ta kara sanyawa man ya ci gaba da faduwa.

Iran dai ita ce kasa ta bakwai a duniya da ta fi fitar da man fetur.