Miliyoyin mutane na fuskantar yunwa a Afrika

Hakkin mallakar hoto Oxfam
Image caption Yara da dama sun tsumbure

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya -WFP ta ce a kalla mutane miliyan 14 na fuskantar barazanar yunwa a kudancin Afrika saboda mummunan fari.

Hukumar ta ce lamarin ya fi muni a kasar Malawi, inda ake tsammanin mutane miliyan biyu da dubu dari takwas ne za su kamu da yunwa, sai kuma kasashen Madagascar da Zimbabwe masu bi mata.

Hukumar ta WFP ta ce a yayin da babu alamun saukowar damuna, akwai yiyuwar lamarin ya kara muni.

Hukumar ta ce daya daga cikin alamun wannan bala'i shi ne yadda ake samun yawaitar yaran da suke fama da rashin abinci mai gina jiki.

Hukumar ta ce yadda yara suke tsumburewa a kasashen Madagasar da Malawi da Mozambik da kuma Zambia na cikin mafi muni a duniya