Friends Reunited zai rufe shafinsa

Shafin Friends Reunited
Image caption Shafin ya gaza cimma takwarorinsa na sada zumunta da muhara.

Shafin sada zumunta da muhara na farko a Birtaniya wato Friends Reunited, ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba zai rufe shafin.

Daya daga cikin wadanda suka kirkiri shafin, Steve Pankhurst, ya yi bayani a wani sakon email cewa har yanzu ana amfani da shafin, amma an daina amfani da ainahin manufar da ta sanya aka bude shi.

A shekarar 2000 ne mai gabatar da shiri na ITV ya bude shafin na Friends Reunited akan kudi Dala miliyan 250.

To sai dai kuma shafin ya gagara gogawa da sauran shafukan sada zumunta na Internet.

A shekarar 2009 ne aka saida kamfanin ga wani mai yin zane-zane DC Thompson akan kudi Pam miliyan 25, daga baya kuma Mr Pankhurst ya wallafa a shafinsa na Internet wanda ya sayi shafin ya yi musu tallan zai saida musu bayan wasu shekaru.

Mr Pankhurt da abokin kasuwancinsa Jason Porter sun amince su sake gwada shafin a karo na biyu ko Allah ya sa ya farfado.

To amma daga baya sun gano yawancin wadanda suke ziyartar shafin su na amfani da shi ne a matsayin dan aika da sako.

Haka kuma an gano cikin musu ziyartar shafin da kuma suka yi rijista da shi sama da miliyan 10, sun yi hakan ne sama da shekaru 10 da suka wuce, dan haka cikakken bayanan su da suka yi rijista da shi ya zama tsohon yayi.

Dan haka Mr Pankhurst ya ce lokaci ya yi da za a rufe shafin dungurugum.

A bangare guda kuma akwai daddadan labari, dan kuwa Mr Pankhurst ya fara shirye-shiryen bude sabon shafin sada zumunta da muhawara mai suna Liife.