An dakatar da tura danyen mai zuwa Kaduna da Warri

Hakkin mallakar hoto AP

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC ya ce ya dakatar da tura gurbataccen man fetur zuwa matatun mai na Kaduna da Warri ta hanyar bututun mai.

Kakakin NNPC, Ohi Alegbe ya shaida wa BBC cewa an dakatar da turawa ne saboda hare-haren da aka kaddamar a kan bututan mai a yankin Niger Delta a karshen makon da ya wuce.

Sai dai ya ce ana ci gaba da tura danyen man ta hanyar jiragen ruwa zuwa matatun mai na Warri da Fatakwal.

Hakazalika ya kara da cewa, matatar mai ta Kaduna tana danyen mai da za ta iya tacewa har tsawon wasu kwanaki masu zuwa.

A yanzu kuma suna jira ne jami'an tsaro su basu tabbacin cewa za su iya zuwa yankin da aka yi barnar domin gyara bututun man na gurbataccen man fetur da iskar gas da aka lalata.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu tayar da kayar baya sun fasa bututan mai

A cikin watan Disambar bara ne matatun man suka koma aiki bayan shafe lokaci mai tsawo ana yi musu kwaskwarima.

Matatar mai ta Warri na tace mai ganga dubu 125 a kullum a yayin da ta Kaduna ke tace ganga dubu 110.

Harin a kan bututun mai na kawo cikas a yunkurin gwamnatin Najeriya na rage dogaro a kan tataccen mai da ake shigo da shi daga kasar waje.

Tuni jami'an tsaron Najeriya suka ce su na farautar masu tayar da kayar baya da suka kai hare-hare a kan bututan mai a yankin Niger Delta a karshen mako.

Ana zargin an kai hare-haren ne saboda nuna adawa da sammacin da kotu ta bayar na a kama Tompolo.

Sai dai masu tayar da kayar bayan sun musanta zargin hannu a hare-haren.