Jariran da ake haifa ba rai sun fi yawa a Afrika

Image caption Wannan wata makabarta ce ta jariran da ake haifa ba rai a Saliyo.

Wani sabon bincike ya nuna cewa a bara kadai, sama da jarirai miliyan biyu da dubu dari shida ne aka haifa ba rai a a duniya, kuma kashi biyu bisa uku na wannan adadi na faruwa ne a kasashen Afirka.

An wallafa sakamakon wannan binciken ne a mujallar kiwon lafiya mai suna Lancet.

Mujallar ta ce lamarin na da matukar tayar da hankali ganin cewa kusan rabin jariran sun mutu ne a lokacin haihuwa.

Rahoton ya gano cewa za a dauki sama da shekara 100 kafin mata a kasashen hamadar kudu da sahara su iya haifar jariransu lafiya-lafiya kamar yadda takwarorinsu ke yi a kasashen da suka ci gaba.

Kasar da aka fi aka fi haifar jarirai ba rai a duniya ita ce Pakistan.