Boko Haram: Ana cece-kuce tsakanin Nigeria da Kamaru

Image caption Birgediya Janar Rabe Abubakar ya ce kasashen tafkin Chadi na kan bakansu na kawar da Boko Haram.

Hedikwatar tsaron Najeriya ta musanta zarge-zargen cewa gwamnatin kasar ce ta kawo tsaiko wajen soma aikin rundunar hadin-gwiwar sojojin kasashen da ke makwabataka da yankin Chadi domin yakar kungiyar Boko Haram.

Kasashen dai sun amince rundunar ta fara aiki a farkon watan Janairun nan da muke ciki, sai dai a karshen makon jiya wata jaridar kasar Kamaru ta wallafa wani rahoton da ke zargin Najeriya da rashin bayar da cikakken hadin kai ga kafuwar rundunar.

Amma kakakin hedikwatar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Rabe Abubakar, ya shaida wa BBC cewa Najeriya ta bayar da cikakken goyon baya, kamar yadda sauran kasashen suka bayar, wajen kafa rundunar da soma aikinta.

Sai dai ya musanta zargin da ake yi cewa rundunar tana yin tafiyar hawainiya wajen fara aiki:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A cewarsa, "Najeriya ta fara bayar da Dala miliyan ashirin da biyu, kuma su ma sauran kasashen sun bayar da iya bakin kokarinsu. Don haka ban san inda aka samu labarin cewa akwai baraka tsakanin wadannan kasashe ba".