Buhari ya gargadi kamfanonin waya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A shekarar da ta gabata ne hukumar NCC ta ci kamfanin MTN tarar kudi mai yawa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi kamfanonin wayar sadarwa na kasar da cewa ka da su bari riba ta yaudare su fiye da mayar da hankali kan tsaron kasa.

Shugaba Buhari ya yi wannan gargadi ne a ranar Talata a Abu Dhabi, babban birnin kasar hadaddiyar daular Larabwa, yayin ziyarar da ya kai kasar.

A lokacin da yake ganawa da 'yan Najeriya mazauna birnin, shugaba Buhari ya ce za a iya nasara ne a kan yaki da ta'addanci kawai idan dukkan masu ruwa da tsaki suka bayar da goyon baya.

Ya bayyana cewa yin rijistar dukkan layukan wayar da ake amfani da su a kasar zai taimaka wa hukumomin tsaro kwarai wajen daukar matakin dakile hare-haren ta'addanci.

Shugaban ya kara da cewa dole ne kamfanonin waya su bi dokokin hukumar sadarwa ta kasa NCC.

A cikin shekarar da ta gabata ne hukumar NCC ta ci tarar kamfanin sadarwa na MTN miliyoyin daloli sakamakon kasa kammala rijistar mutanen da suke amfani da layukan wayar kamfanin.