Tattalin arzikin China ya tabarbare

Shugaba Xi Jinping Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption China na daga sahun gaba na kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.

Tattalin arzikin kasar China ya habaka da kashi 6.9 bisa dari a bara, kuma ita ce habaka mafi kankanta da tattalin arzikin ya yi a shekaru ashirin da biyar da suka wuce.

Haka kuma an samu jinkirin fadadar tattalin arzikin da kashi 6.8 bisa dari.

Lamarin dai bai tayar da hankali ba a kasuwannin Asiya, kasancewar an yi tsammanin haka.

Damuwar da ake yi game da makomar tattalin arzikin Chinar, ciki har da raguwar bukatar kayan da kasar ke samarwa da faduwar darajar kudin kasar, duka sun taimaka wajen faduwar darajar hannayen jari a kasuwannin duniya a bana.

Wadannan alkaluma dai na yi wa kasar Sin din matsin-lamba domin ta dauki matakan tallafa wa tattalin arzikin.