Jirgi maras matuki ya dira kan motar da ke tafiya

Image caption jirgin sama marar matuki

Wasu kwararru a Jamus sun koya wa wani jirgi mai sarrafa kansa yanda zai sauka a kan motar da ke tafiya.

Masanan, wadanda jami'ai ne a cibiyar nazarin sararin samaniya ta Jamus sun jarraba wani jirgin sama marar matuki ne, wato drone, inda ya gwada sauka a cikin wata raga a kan wata mota mai tafiyar kilomita 75 a cikin sa'a guda.

Kwararrun sun ce za a iya sarrafa da fasahar da suka yi amfani da ita wajen kira jiragen sama marasa matukan da ba su da tayu, wadanda za su iya dadewa a sararin samaniya na wani tsawon lokaci.