Ghana ta kara tsaro a iyakarta

Shugaba John Mahama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matakin ya biyo bayan harin da aka kai Burkina Faso.

Ghana ta ce ta fara tsaurara tsaro a kan iyakarta da kasar Burkina-Faso don hana 'yan ta'adda shiga cikin kasarta.

Hakan dai ya biyo bayan harin ta'addancin da aka kai ne a Burkina Fason, inda aka kashe mutane sama da ashirin.

Ministan cikin gida mai barin gado, Mark Woyongo, ya ce za a kuma tsaurara matakan tsaro a wuraren taron jama'a.

Za kuma kara tsarara matakan tsaro a arewacin kasar, saboda harin da aka kai kasar Burkina Faso alamu ne da ke nuna ya kamata su kara sanya ido kan iyakokinta.

Tun dai lokacin da Ghana ta karbi fursunonin Guontanamo, masu sharhi kan al'amuran tsaro ke cewa matakin zai yi barazana ga tsaron kasar.