IS: Jihadi John ya mutu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mohammed Emwazi da aka fi sani da Jihadi John

Kungiyar IS ta tabbatar da mutuwar wani mayakinta da aka fi sani da Jihadi John.

Cikin wata mujallarta ta intanet, kungiyar ta ce an halaka Jihadi John ne a wani harin da aka kai masa da jirgin sama marar matuki a Rakka, kuma wannan labarin ya tabbatar da ikirarin da Amurka ta yi a baya cewa an kashe mayakin kungiyar IS din.

Jihadi John dai mutumin Burtaniya ne dan asalin Kuwaiti, kuma ya sha fita a cikin hotunan bidiyon kungiyar IS, musamman idan ake halaka 'yan jarida da masu aikin agaji da kuma sojojin gwamnatin Syria.

A bangare guda kuma, kungiyar IS din ta ce tana shirin rage albashin mayakanta zuwa rabin abinda ta saba biyansu, matakin zai shafi dukkan 'ya'yan kungiyar.

Kungiyar dai ta bayyana cewa daukan matakin ya zama wajibi saboda ta shiga wani hali, kodayake wakilin BBC ya ce watakila kungiyar na fama da matsi ne irin na rashin kudi sakamakon hare-haren da aka kai kan matatun man da ke karkashin ikonta.