An zargi shugaban Nijar da karya dokar zabe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Isufu na daga cikin 'yan takarar shugabancin Nijar a zaben Fabrairu.

Jam'iyyun adawa a jamhuriyyar Nijar na zargin shugaban kasar Alhaji Mahamadu Isufu da soma yakin neman zabe tun lokacin bai yi ba.

Wasu 'yan takara a zaben shugaban kasar ne suka yi wannan korafi, suna masu cewa hakan ya saba wa dokar kasa.

A kwanakin baya ma sun kuma zargi shugaba Isufu kuma dan takaran jam'iyar PNDS Tarayya, da cewa ya yawaita yin taruka daga wannan gari zuwa wancan inda yake jan hankalin magoya bayansa game da zaben mai zuwa.

A watan Fabrairu ne za a yi zaben shugaban kasa a jamhuriyyar Nijar.