Lassa na kara bazuwa a Nigeria

Image caption Bera ne ke yada cutar Lassa.

Gwamnatin Najeriya ta ce a halin yanzu daukacin jihohin kasar 36 na cikin hadarin samun bullar zazzabin Lassa mai kisa.

Da yake jawabi yayin wani taron gaggawa na majalisar koli ta harkokin lafiya ta kasar a ranar Talata, ministan lafiya Farfesa Isaac Adewale, ya ce a halin yanzu cutar ta bazu zuwa jihohi 17 na kasar.

Farfesa Adewale ya ce tuni aka tura tawagogi na musamman zuwa dukkan jihohin kasar domin binciken halin da ake ciki.

Kazalika, an samar da kwamitin kasa na yaki da cutar Lassa kuma ministan lafiyar ya sha alwashin kawar da cutar nan ba da dadewa ba.

Zuwa yanzu dai mutane 112 ne suka kamu da cutar Lassa, yayin cutar ta hallaka mutane 72.