"Majalisar dokokin Nigeria ta gaza kan harkar tsaro"

Image caption An zargi 'yan majalisa da rashin mayar da hankali kan harkar tsaro.

Kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci da rashawa a duniya, ta ce gazawar majalisar dokokin Najeriya wajen sa ido a kan bangaren tsaro ne ya haddasa almundahanar da ta yi kafar ungulu ga yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.

A wani rahoto da ta fitar ta hannun kungiyar CISLAC, mai sa ido a kan ayyukan majalisun dokoki a Najeriya, kungiyar ta Transparency International ta ce babu inda alakar cin hanci da rashawa da matsalar tsaro ta bayyana a duniya kamar a Najeriya.

Rahoton ya kuma ce ko da yake Shugaba Muhammadu Buhari ya fara daukar kyakkyawan matakin yaki da cin hanci da rashawa, kame tsoffin jami'ai kawai bai wadatar ba.

'Yan majalisar dokoki a Najeriya dai sun sha kare kansu daga zargin gazawa wajen tabbatar da ana yin abin da ya dace a bangaren tsaro da cewa su alhakin da ya rataya a wuyansu shi ne yin doka, tabbatar da aiki da ita alhakin bangaren zartarwa ne.