Dubai za ta mayar wa Nigeria kudaden da aka sace

Hakkin mallakar hoto Femi Adesina
Image caption Shugaban Nigeria da na Dubai sun cimma yarjejeniya da dama

Kasar hadaddiyar daular Larabawa, UAE ta amince ta dawo wa Najeriya kudaden da wasu 'yan kasar suka sace, sannan suka boye a bankunan kasarta.

UAE ta amince ta mayarwa Najeriya kudin ne bayan mahukuntan kasar sun sanya hannu da tawagar Najeriya a kan yarjejeniya shida domin karfafa alakarsu, a ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi kasar.

Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami, da takwaransa na UAE Sultan Bin Saeed Albadi ne suka wakilci kasashensu wajen sanya hannu kan yadda za a dawo da kudaden da aka sace daga Najeriya aka boye a bankunan Dubai.

Kazalika, sun kuma sanya hannu kan yadda za a mayar da mutanen da ake zargi da laifi, da taimakawa juna kan yadda za a shawo kan matsalolin aikata miyagn laifuka.

Anar zargin wasu tsofaffin jami'an gwamnatin Najeriya da boye kudaden da suka sata a bankunan kasashen Turai da na Larabawa, kuma shugaba Buhari ya sha alwashin kwato kudaden, sannan ya daure mutanen da suka sace su.

Yarjejeniyar ta kuma hada da kasuwanci inda ministar kudi ta Najeriya Mrs Kemi Adeosun, da takwaranta na UAE Obaid Attayar, suka sanya hannu kan yarjejeniyar hana ninka karbar kudin shiga.

Dukkan wadannan yarjejeniya an yi su ne tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da mai jiran gado na UAE, Sheikh Mohammed Bin Zayed Al Nahyan.