'Yan bindiga sun kai hari jami'ar Pakistan

Mayakan Taliban Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kawo yanzu babu kungiyar da aka sanar ta dauki alhakin kai harin.

'Yan bindiga sun far wa wata Jami'a da ke arewa maso gabashin kasar Pakistan, inda har yanzu ake ci gaba da musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da ke gadin jami'ar da kuma 'yan bindigar.

Motocin yaki sun yi wa jami'ar Bacha Khan mai dalibai 3000, kawanya da ke gundumar Charsadda mai nisan kilomita Hamsin da birnin Peshawar.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wani Farfesa masanin kimiyyar sinadarai ya rasa ran sa, wasu mutane 50 kuma sun ji rauni.

Tuni aka kwashe dalibai da malamai daga jami'ar. A shekarar 2014 mayakan Taliban sun hallaka fiye da dalibai 150 a wata makaranta da ke birnin Peshawar.