Shin ka san jari bola sana'a ce mai ci?

Mustafa Hamdan matashi ne mai zafin neman na kansa.
Bayanan hoto,

Mustafa Hamdan matashi ne mai zafin neman na kansa.

Mostafa Hemdan na kokarin ganin ya samu rufin asirin rayuwa ta hanyar yin sana'ar Jari Bola, amma fa babu wata nasara da ke samuwa ba tare da fadi-tashi ba.

Mustafa dan shekara 25, shi ne mamallakin kamfanin Egyptian Recyclobekia, irinsa na farko a Gabas ta Tsakiya da yake sake sarrafa kayayyakin lantarki da suka daina aiki.

Ya samar da kamfanin ne shekaru biyar da suka gabata, inda ya mayar da garejin ajiye motoci na gidan iyayensa wajen aikinsa, wanda ke garin Tanta mai nisan kilomita 90 daga arewacin Al-Kahira, babban birnin Masar.

A lokacin da Mustafa yake karatun Injiniya, shi da wasu dalibai 19 suka shiga gasar matsakaitan sana'o'i da ake kira Injaz Egypt.

An ware dala 10,000 a matsayin kyauta domin taimaka musu wajen samar da tunanin irin kasuwancin da za su yi.

Mustafa ya samu basirar irin kasuwancin da zai yi ne sakamakon wani shiri da ya kalla a talabijin.

Ya ce, "Ina kallon wani shiri a kan sake amfani da kayan lantarki da suka daina aiki don samar da wasu abubuwan, sai na fahimci cewa akwai damarmaki da yawa wajen samar da karafa daga abubuwa da yawa."

Ya kara da cewa, "Sana'a ce mai ci sosai a Turai da Amurka, amma babu wanda ke yin ta a Gabas ta Tsakiya."

Bayanan hoto,

Mustafa ya ce jari bola sana'a ce mai ci da rufin asiri.

A wannan lokacin ne ya samu basirar samar da wannan kamfani na Recyclobekia, kuma da wannan ne Mustafa ya samu nasarar lashe gasar.

Sunan kamfanin ya samo asali ne daga kalmar Larabci ta "roba bekya", wacce take nufin "tsofaffin kaya", kuma kalma ce da ake yawan jin ta a kan titunan Masar inda mutanen da aka fi sani da 'yan gwan-gwan ke yawan amfani da ita wajen neman sayan tsofaffin kayayyaki na amfanin gida.

A yau, wannan matashin dan kasuwa na Masar ya dauki ma'aikata kimanin 20 da suke masa aiki a kamfaninsa mai rassa hudu, yana kuma sayar da tsofaffin kayan wuta na kimanin dala miliyan 2.4 duk shekara.

A cikin wannan hali dai, Mustafa ya samu nasara, duk da kalubalen da ya fuskanta da suka hada da tashe-tashen hankulan da aka yi ta samu a Masar.

"Cinikin farko"

A lokacin da aka fara wannan kasuwanci a shekarar 2011, wanda ya yi daidai da lokacin da aka fara juyin juya hali a Masar, Mustafa ya fara kasuwancin ne ta hanyar tallata hajarsa a wani shafin kasuwanci na intanet.

Daga nan ne kuma aka fara yi wa kamfanin Recyclobekia cinikin farko, inda wani mutum daga kasar Hong Kong ya sayi rumbun adana bayanai na komfuta har tan 10.

Mustafa ya ce, "A wannan lokacin ban ma san a ina zan samu wannan kaya mai yawa haka ba, amma dai sai na amince."

Bayanan hoto,

Kayayyaki irin su tsoffin komfutoci da kayan lantarki na yin kasuwa sosai

A kokarinsa na samun tsofaffin kayan lantarki sai ya koma Al-Kahira babban birnin kasar, inda miliyoyin mazauna birnin ke zubar da kimanin tan 15,oo na tsofaffin kayayyaki.

Ya fahimci cewa yana bukatar kimanin dala 15,000 don aikewa dan kasar Hong Kong kayan da ya bukata, amma lokacin bai samu wannan kudi na gasar Injaz Egypt ba.

A kan haka ne yayi kokarin gamsar da wani Farfesa na jami'a don ya bashi rance, da sharadin zai bashi kashi 40 cikin 100 na ribar da ya samu.

Bayan watanni hudu kuwa sai hakarsa ta cimma ruwa, ya samu aikewa wannan mutum da kayan nan.

Duk da cewa ya fuskanci kalubale daban-daban, Mustafa bai yi kasa a gwiwa ba, don yanzu haka kamfaninsa na mu'amala da kamfanoni da dama na kasashen ketare musamman Turai, inda suke sayen tsofaffin kayan wuta a wajensa.