'Yan ci-rani: Kotu ta amince da shawarar Obama

Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu suka dai na cewa Mista Obama ya wuce gona da iri a ikon da ofis dinsa ya bashi.

Kotun Kolin Amurka ta amince da sake duba shawarar da shugaba Obama ya yanke ta gaban kansa, kan sauya manufofin gwamnati akan 'yan ci_rani, domin bai wa miliyoyin wadanda basu da takarda damar zama a Kasar.

Shugaban ya sanya hannu a kan wata doka a shekarar 2014 game da hakan, amma wasu kotuna a jihohin da 'yan Republican ke mulki suka ce sam basu amince ba.

Masu suka dai na cewa Mista Obama ya wuce gona da iri a ikon da ofis dinsa ya bashi.

Ana tsammanin yanke hukunci wuraren watan Yuni, lokacin da Amurka take tsakiyar yakin neman zabe inda batun 'yan ci-ranin zai zama wani babban batu.